Labarai
Matakin haramta kiwo barkatai da wasu gwamnoni suka dauka ya sabawa doka – Buhari
Fadar shugaban kasa ta ce matakin da gwamnonin kudancin kasar nan suka dauka na haramta kiwo barkatai a jihohinsu ya sabawa doka.
Babban mataimakin na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce duk wani dan Najeriya yana da ‘yancin watayawa a ko ina a cikin kasar nan ba tare da la’akari da Jihar da ya fito ba, kuma babu bukatar haramta kiwon sakamakon matakan da shugaban kasa ya samar don magance rikice-rikicen makiyaya da manoma a Najeriya.
Ta cikin sanarwar, Malam Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya amince da shawarwarin da ministan harkokin noma Alhaji Sabo Nanono ya bayar ta cikin rahoton da ya mikawa shugaban kasar, kuma shugaban ya sanya hannu a kai a cikin watan Afrilun jiya.
You must be logged in to post a comment Login