Ƙetare
Matakin Isra’ila na tilasta wa Falasɗinawa ficewa daga sansanonin ƴan gudun hijira laifin yaƙi ne- Human Rights Watch

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana matakin Isra’ila na tilastawa Falasɗinawa ficewa daga sansanonin ƴan gudun hijira uku da ke gaɓar yamma da kogin Jordan da ta mamaye a matsayin laifin yaƙi.
Sama da Falasɗinawa da dubu talatin ne dai daga Jenin da Tulkarem da Nur Shams aka ba su umarnin ficewa daga gidajen su a watan Janairu da Fabrairu yayin wani farmakin da sojojin Isra’ila suka kai.
Tun daga lokacin ba a bari sun koma gidajensu ba, kana an ruguza daruruwan gidajen domin samar da sabbin hanyoyin shige da ficen sojoji.
Isra’ila ta ce tana tarwatsa abubuwan da ta bayyana a matsayin kayayyakin ayyukan ta’addanci ne a sansanonin.
You must be logged in to post a comment Login