Labarai
Matasa su dage neman ilimin fasahar zamani – Arewa Agenda
Wata Kungiya mai rajin tallafawa matasa a nan Kano mai suna Arewa Agenda, ta yi kira ga matasa da su dage wajen neman ilimin fasahar zamani domin samun sana’o’in dogaro da kai.
Daraktan kungiyar Alhaji Muhammmad Dahiru Lawan ne ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a nan Kano.
Alhaji Muhammad Dahiru ya kuma ce matasan Jihar Kano suna da bukatar ilimin fasahar zamani, sakamakon wasunsu suka gaza gano hanyoyin bi domin samun sana’o’i na zamani a ciki.
Ya kara da cewa an bar arewacin kasar nan a baya a bangaen bunkasar fasahar zamani, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda wasu sassan kasar nan suka samu ci gaba a fannin.
Wakilinmu Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa kungiyar ta bukaci kafafen yada labarai da na intanet da su yi kokarin wayar da kan matasa hanyoyin da ya kamata su bi wajen bunkasa fasahar zamanin.
You must be logged in to post a comment Login