ilimi
Matasa su guji amfani da social media sakaka- Iyaye
Shugaban Kungiyar iyayen yara reshen Makarantar Khadija Memorial college dake Kan titin Ahmad Musa a unguwar Hotoro yayi Kira ga matasa da su Kula da kafafen aada zumuntar da ake dasu na kafar Internet.
Alhaji Muhammad Isyaku yayi wannan Kiran ne yayin bikin yaye dalibai na Makarantar Khadija Memorial College din ne a yau, Daya gudana a ShopRite.
Alhaji Muhammad Isyaku ya ce ‘gurbata tarbiyar da social media take yi musamman ma ga matasa yasa Khadija Memorial College ta Sanya Ido sosai akan dalibanta, wajen ganin iyayensu Basu sakar musu wayoyin ko Wani Abu da zai Basu damar amfani da social media ba’.
Da yake jawabi yayin bikin yaye daliban, Sarkin Sudan din ringim Alhaji Abubakar Mahmud Kira yayi ga iyayen dasu dage wajen tabbatar da sun bawa ‘ya’yansu ilimi Mai amfani.
Wanda ya ce ‘a halin da ake ciki a yanzu bayar ga ilimi ga ‘ya’ya shine kadai mafitar da suke da ita a yanzu’.
A hannu guda Mai Makarantar ta Khadija Memorial Malam Muhammadu Adamu cewa ‘yayi a irin wadannan ranakun na yaye dalibai suna zama don zakulu kura-kuransu, tare Kuma da Nemo hanyar ciyar da ilimin daliban Makarantar gaba’.
Daliban da aka yaye su 152 a wannan karon a Khadija Memorial College, daya zamo Karo na 8, sunyi alkawarin zamowa jakadu na gari a duk Inda suka samu kansu a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login