Labarai
Matasa su yi riƙo da sana’o’in hannu – Falakin Shinkafi
An yaye ɗalibai 50 da suka koyi sana’o’in dogaro da kai a ƙaramar hukumar birni.
Falakin Shinkafi Ambasada Yunusa Hamza ne ya ɗauki nauyin koyar da matasan kan dabarun kasuwanci ta intanet.
An gabatar da taron ne a makarantar sakandire ta Rimi City da ke unguwar Yakasai.
A yayin taron Ambasada Hamza ya yi kira ga matasan kan su yi amfani da abin da suka koya.
Ya ce, a yanzu sana’o’in dogaro da kai su ne mafita ga matasa la’akari da matsalar rashin aikin yi da ta ta’azzara.
Labarai masu alaka:
An naɗa Ambasada Yunusa Hamza a matsayin Falakin Shinkafi
Hukuncin kisa ne ya fi dacewa ga masu yin ɓatanci – Amb. YY Hamza
Wasu cikin waɗanda suka amfana sun yi godiya tare da nuna farin cikinsu.
Taron ya samu halartar mutane da dama da suka haɗar da shugabannin al’umma da ƙungiyoyi.
You must be logged in to post a comment Login