Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matashin da ake zargi da ƙwacen waya ya mutu- Yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar matashin nan da ake zargi da aikata fashi da makami ta hanyar amfani da Danbuda wajen yiwa wata mace kwacen waya akan titin Zoo Road a karshen makon jiya.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar yau Talata.

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, matashin ya mutu ne da sanyin safiyar yau Talata a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.

Tunda da fari dai Matashin ya kwace wayar wata mata ne, bayan ya yi mata barazana da Dan-buda, kuma a kokarinsa na tserewa ne mota ta taka shi ta karya masa kashin gadon baya da kuma wani mummunar rauni akan sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!