Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun hallaka yan bindiga a Zamfara

Published

on

Rundunar sojin saman Nijeriya hadin gwiwa da dakarun Operation Hadarin Daji, sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga goma sha biyu, ciki har da wasu manyan jagororinsu a jihar Zamfara.

Dakarun sun samu nasarar ne a wani farmaki da suka kai ta sama.

Ta cikin wani rahoto da rundunar ta fitar, ta bayyana sunayen Ado Aliero da Dan Karami a matsayin shugabannin ‘yan ta’addar da suka rasa rayukan na su.

Da yake karin bayani game da nasarar da suka samu, mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce, babban hafsan rundunar Air Marshall Hassan Abubakar ya kuma ba da umarnin sake karfafa ayyukan rundunar a yankin baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!