Labarai
Matawalle ya dakatar da dagacin da ke sayarwa ‘yan bindiga makamai
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da dagacin garin Badarawa da ke masarutar Shinkafi, Surajo Namakka sakamakon samun-sa da aka yi da sayarwa ‘yan ta’adda makamai.
Matawalle ya ce, bazai lamunci ayyukan ta’addanci ya ci gaba da faruwa a jihar ba.
An dai sanar da dakatar da dagacin ne a yau juma’a, wanda daraktan yada labaran gwamnan jihar Yusuf Idris ya fitar ya kuma rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin an kama shi ne lokacin da ya ke mika makamai ga wani mai suna Kabiru Bashiru dake garin Maniya a masarautar Shinkafi, har ma ya karbi wani kaso daga cikin kudi na naira N100,000.
You must be logged in to post a comment Login