Labaran Kano
Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta
Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu ya ja hankalin mutane da suke kalubalanta magangannu da yake kan kare hakkin mata, da su koma makaranta don samun cikakken ilimin addinin Islama.
A cewarsa duk maganar da yake tana da tushe a mahangar addini Islama.
Malam Muhammad Sunusi na biyu ya bayyana haka ne lokacin kaddamar da litattafai Uku da Hajiya Mariya Inuwa Durimin Iya ta wallafa kuma aka kaddamar a yau.
Ya kuma kara da cewa musulunci yazo da doka da tsari a rayuwar aure kuma ana gina rayuwar ne bisa kauna da tausayi da suke zama a matsayin rayuwar aure.
A nasa bangaren Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa yawancin matsalolin da suke faruwa a gidajen aure , mafi akasari maza ne keda kaso mafi yawa daga ciki.
Farfesa Isah Mukhtar malami a sashen koyar da harsunan Najeriya a jami’ar Bayero ta kano ya bayyana litattafan da Hajiya Mariya ta wallafa a matsayin mabudin na kawo sauyi a rayuwar malaman Bahaushe musamman a litafin ta mai suna Almajiri Da Bara.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa marubuciyar ta nuna godiyar ta ga Allah sanan ga mutanen da suka hallaci taron tare da yin kira ga makarantun dasu bubiyi litattafan nata da idanun basira.