Kasuwanci
Matsin rayuwa: Za mu fara bankaɗo masu ɓoye kaya – Barista Muhuyi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano, ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da duk wani ɗan kasuwa da aka samu da laifin ɓoye kaya a wannan lokaci.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai ranar Alhamis a ofishinsa.
Ya ce, tuni shirin su ya yi nisa na fara bincike tare da kama duk waɗanda aka samu laifin ɓoye kaya, la’akari da matsanancin halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki a yanzu.
“idan ba ku manta ba, a duk lokacin da Azumi ya gabato ana samun wannan matsala, amma wannan hukuma ta mu muna yin tsayin daka wajen kawo ƙarshen matsalar, to yanzu haka ba za mu bari ba” a cewar Muhuyi.
Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya tabbatar da cewa, hukumarsu za ta kawo ƙarshen matsalar nan ba da daɗewa ba, kasancewar haƙƙin gwamnati ne ta kula da haƙƙin al’ummarta.
You must be logged in to post a comment Login