Connect with us

Labarai

Mawaƙi kuma Jarimin fim Jimmy Cliff ya mutu ya na da shekaru 81

Published

on

Shahararren mawaƙi kuma ɗan fim, wanda kuma ya taimaka wajen ɗaukaka kiɗa da waƙoƙin Reggae Jimmy Cliff ya mutu yana da shekara 81.

An haife shi a ranar 30 ga watan Yuli 1944 a St. James Parish na ƙasar Jamaica, kuma ya mutu ranar 24 ga watan Nuwamban 2025 a babban birnin ƙasar Jamaica wato Kingston.

Wani saƙo da matarsa Latifa Chambers ta wallafa ɗazu a Instagram na cewa, “Cikin matuƙar jimami make sanar da ku cewa mijina Jimmy Cliff, ya rasu a sanadiyyar matsalar rashin lafiya ta haƙanniya wato ciwon huhu.”

Ƴaƴansu Lilty da Aken sun sanya hannu a ƙasan sanarwar.

Cikin fitattun waƙoƙinsa, akwai “You Can Get It If You Really Want” da “I Can See Clearly Now” da kuma “Wonderful World, Beautiful People”.

Ya kuma fito a fina-finai, ciki har da fim ɗin “The Harder They Come” wanda ya fito a 1972.

Jimmy Cliff na cikin mawaƙa ƙalilan – ciki har da Bob Marley – da aka karrama da lambar yabo ta Jamaican Order of Merit.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!