Kasuwanci
Mayar da Kamfanin NNPC mai zaman kan sa, na nufin za a daina bada tallafin man fetur a Najeriya – Dakta Abdurrazaƙ Fagge
Shugaban Sashen nazarin tattalin arziƙi a jami’ar Yusif Maitama Sule a nan Kano, Dakta Abdurrazaq Ibrahim Fagge ya ce sabon shirin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari akan kamfanin NNPC na nufin nan gaba gwamnati ba za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.
Dakta Abdurrazaq Ibrahim Fagge ya bayyana haka a zantawar sa da Freedom Radio.
“Wannan mataki da shugaba Buhari ya ɗauka na bai wa kamfanin mai na ƙasa NNPC damar jawo masu zuba hannun jari a kamfanin abu ne da ke nuni da cewa ƙasar ba za ta ci moriya ba ta fuskar samun kuɗin shiga” a cewar Fagge.
“Wannan matakin ba zai sauya yadda kamfanin yake a baya ba, sakamakon cewa wadanda za su jagoranci kwamitin sabon kamfanin sune dai suke aiki a hukumar”.
Dakta Fagge ya ƙara da cewa “Duk lokacin da aka samu tsadar mai, kamfanin NNPC ƙarƙashin gwamnatin tarayya na ƙoƙarin ba da tallafin ga al’umma, amma mayar da kamfanin NNPC mai zaman kan sa na nuni da cewa nan gaba kaɗan duk wani ɗan Najeriya zai ɗanɗana kuɗarsa”.
A karshen mako ne dai shugaba Buhari ya amince da naɗa daraktocin da za su jagoranci gudanarwar kamfanin.
Wanda Sanata Ifeanyi Ararume yake shugaba, sai Mele Kyari a matsayin shugaban Kwamitin, yayin da Umar Ajiya yake babban daraktan da ke kula da harkokin kuɗi.
Sai kuma sauran mambobin da suka haɗar da Dakta Tajuddeen Umar da Misis Lami Ahmed da Mallam Mohammed Lawal da Sanata Margaret Chuba Okadigbo da Barista Harry Marshal da kuma Cif Pius Akinyelure.
You must be logged in to post a comment Login