Connect with us

Labarai

Mazauna Dakata da kewayenta sun yi tattakin lumana na neman daukin gwamnati Kano

Published

on

Mazauna unguwar Dakata da kewayenta, sun gudanar da tattakin lumana na ankarar da gwamnatin jihar Kano, mahukunta kama daga ‘yan Majalisar Jiha da Tarayya dangane da yi ko gyaran  Titin Kwanar Kotu ta Jigirya zuwa Dakata Police Station da Kwanar Layin Isma’ila Mai Biscuit.

 

Tattakin ya gudana a yammacin jiya  Lahadi karkashin jagorancin kungiyiyon  gwagwarmaya  na matasan yankin da suka taka tun daga kwanar  Kotu har zuwa Dakata Police station.

 

Ya yin tattakin matasan dauke da Kwalaye sun bayyana cewar hanyar ta dade tana ci musu Tuwo a kwarya sakamakon mummunar lalacewar  da ta yi duk da muhimmancin  ta na hada bangarorin unguwannin da dama da tayi tare da  manyan ma’aikatu da masana’antu da ke bangaren.

 

Da ya ke jawabi a ya yin gangamin shugaban gamayyar matasan da suka gudanar da tattakin koken , Muhammad Auwal, ya ce sun shirya gangamin ne domin kira ga mahukunta.

 

Dumbin matasan yankin na Dakata, da suka fito daga yankin Sabuwar Dakata da Tsohuwar Dakata, sai Jigirya , da Kawaji da yankin Yankaba ne suka fito gangamin tare da gudanar da tattakin don isar da sakon su ga hukumomi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!