Labarai
Kotu ta yanke wa fitacciyar ‘yar TikTok hukuncin ɗaurin shekara 1 a gidan Yari

Kotu a birnin Accra na ƙasar Ghana ta yanke wa wata fitacciyar ‘yar TikTok mai suna Camilla Alhassan, hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari tare da yin aikin wahala, bayan samun ta da laifin yaɗa labaran ƙarya da kuma cin mutuncin tsohon Shugaban kasar John Dramani Mahama, a shafukan sada zumunta.
Camilla Alhassan mai shekaru 43, ta wallafa wasu bidiyoyi a shafinta na TikTok tana iƙirarin cewa John Mahama ya yi tsafi da shanu guda 32 domin ya lashe babban zaɓen ƙasar na shekarar 2024.
Ta kuma ƙara da cewa tallafin audugar Mata da aka raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a yayin yakin neman zaben wancan lokaci na da alaƙa da wannan tsafi.
A lokacin shari’ar, Camilla ta amsa laifukan da ake tuhumarta da su na yaɗa labaran ƙarya da kuma kalaman kiyayya da za su iya tayar da tarzoma.
You must be logged in to post a comment Login