Labarai
NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol fiye da guda miliyan 1 da rabi

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta ce ta kama kwayoyin Tramadol sama da miliyan 1 da dubu dari biyar da aka boye a cikin wasu manyan tireloli biyu.
Haka zalika hukumar ta ce ta samu nasarar cafke wasu da ake zargi mambobin wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi ne da ke gudanar da harkokinta tsakanin kasar Togo da Jamhuriyar Benin zuwa nan Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce nasarar ta biyo bayan wani aikin binciken sirri da suka gudanar kan wata Mota.
Babafemi ya ce a ranar 2 ga Yulin da muke ciki ne jami’an NDLEA suka tare daya daga cikin tirelolin a kan titin Lagos zuwa Ibadan, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano.
You must be logged in to post a comment Login