Labarai
Mazauna Tokarawa sun yi kururuwar neman dauki
Mazauna garin Tokarawa dake yankin karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, sun koka tare da yin kira ga gwamnatin jihar kano kan ta kawo musu dauki bisa lalacewar makarantun firamare da sakandaren tare da matsalar wutar lantarki da garin ke fama da shi.
Mutanen garin sun ce, shekaru da dama kenan suna fama da wannan matsala ta makaranta a garin har ma da zaizayar kasa da sauran wasu tarin matsaloli.
sun kara da cewa daliban makarantar a kasa suke zama ga rashin malamai da suke fama da shi duk kuwa da cewa akwai tarin kamfanoni masu zaman kansu a garin, amma ba su cika tallafa musu ba.
Kan wannan koke ne Freedom Radio ta tuntubi Dagacin garin na Tokarawa Malam Yakubu Usman, wanda ya ce suna kokari wajen ganin shugabannin karamar hukumar nassarawa sun kawo musu dauki domin saukaka musu wahalhalun da suke sha musamman daliban makarantun firamare da na sakandare.
Haka kuma Dagacin, ya kara da cewa sun kai wa kamfanonin da ke makwabtaka da su takardu domin su taimakawa makarantun da kayan aiki na zamani.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa Al’ummar suna kira da masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati da ta kawo musu dauki a garin.