Sharhi
Me yasa ‘’yan Najeriya ke cikin matsanancin talauci?
A kullum yanayin talauci a Najeriya karuwa yake ,musamman ma tsakanin mata a arewacin Najeriya.
Hakan yasa abubuwa suke ta kamari ba tare da shawo kan lamarin.
Matsalar Talauci a Najeriya musamman ma anan Arewa na karuwa babu kaidi ,wannan yasa wasu masana ke alakanta laifuffuka dake faruwa a yau da gobe a sassan kasar nan da Talauci.
A kullum al’ummar Najeriya karuwa suke yi .amma tattalin arzikin kasar baya karuwa dai dai da yawn mutanan kasar.
Ko kwanakin baya akwai wata kididdiga da kungiyar OXFAM ta fitar tace tsabar kudi na karuwa a Najeriya amma har yanzu mutanan kasar na kara fatara.
Kungiyar ta Oxfam tace a yanzu wasu tsirarun yan Najeriya sun mallaki fiye da dala Biliyan ashirin da tara, amma duk da haka sauran yan kasar rashin abun yi na karuwa.
Haka a wani taron tattalin arziki da ya gudana a jamiar Bayero taron ya bayyana cewa kimanin al’umma a jahar Kano sn kai miliyan uku da suke tashi da safe basu da gurin da zasu je.
Wannan kididdigar ta tayar da hankalin masu hankali da wadanda suke ganin ya kamata a zauna lafiya, amma ta yaya zaa magance matsalar ,hakan ya sa wasu ke ganin idan har zaa samu wadanda sun kai miliyan uku basu da inda zasu to idan baa yi maganin matsalar ba hakan zai ta karuwa ba kakkautawa .
Idan har yanzu akwai mutum miliyan uku da basu san inda zasu ba to ta yaya zaa yi kenan anan gaba.
Daga cikin wadanda kididdigar take nunawa cewa wasu daga cikin wadanda mata a arewacin Najeriya na fuskantar matsalar ta talauci .
Rahotanni na nuni da cewa saboda rashin kokarin wasu mazaje a arewacin Najeriya mata ne suke yin aikatau domin daukar nauyin iyali.
Wannan ya hada da damuwar su ta biyan kudaden makaranta ga yayan su da sauran fadi tashi na harkar iyalin su .
A wata kididdigar da aka fitar a kwanakin baya akwai yan Najeriya fiye da miliyan 86 da suke zauna cikin matsanancin talauci , wanda a kasashen Duniya itace a gaba.
A yanzu A Najeriya mutane na tashi su kwanta basu da abinda zasu ci ,
Ko a bangaren ma’aikata har yanzu cecekuce ake tayi a game da tsarin nan na biyan mafi karancin albashi na Naira dubu Talatin afadin Najeriya, maaikaci na ta tunanin yaya zaa yi a kara masa albashi.
Wadannan yan Najeriya dake karuwa da suka kai a fiye da miliyan 86 a matsayin wadanda suke rayuwar ,matsanancin talauci abu ne da a Iya cewa kakara kaka.
Domin kuwa wannan shiri Gwamnati take yi na kare tattalin arziki yadda kowanne dan Najeriya zai amfana.
Ko a kwanakinnan ma sai da wasu sassan kasar nan musamman ma nan Kano suka fada cikin matsanancin duhu sakamakon rashin wutar lantarki, amma duk da yawan yan Najeriya fiye da miliyan 86 da suke fama da matsanancin Talauci kasar bata kai ta mallaki guraben ayyukan yi da zata saka mafiya yawan yan Najeriya.
Talaucin da yan Najeriyar ke fama da shi ya kai intahar da wasu kan fita bara ce barace kan tituna da daddare dan kar a gansu da tsoran tozartawa.
Idan ka dawo bangaren kula da lafiyar al’umma yawan yan kasa yasa guraran kula da lafiyar yayi musu kadan ta yadda idan aka samu wata babbar matsala sai dai a cewa mara lafiya yayi hakuri babu gado.
Kai babban abun tashin hankalin shi ne yadda wasu suka rasa kudin magani da zasu yiwa kansu yayin da su da iyalansu suka fada matsanancin rashin lafiya.
Masu sauraron kafafan yada labarai a nan Birnin Kano sun san yadda a cikin shirye shiryen na musamman a ke neman taimakon kudaden kula da lafiyar al’umma sakamakon rashin kudin magani a asibiti.
Masu sauraron ke nan ,su ma’aikatan kafafan yada labaran ma har sun saba , inda gidajen rediyan suka zama tamkara asibitocin, wani abun sai dai mutum ya rufe ido ko yaiyi ta maza amma idan ba haka ba zai iya barkewa da kuka, kuma yawancin mabukatan mata ne , wannan neman taimako da ake yi kafafan yada labarai kai kace babu mahukunta da dukiyoyin al’umma ke hannunsu da ya hada da yan majlisun