Kiwon Lafiya
Meke hadassa Tabin hankali ?
Binciken da hukumar lafiya ta duniya ta yi ya, ya nuna cewar Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake fama da masu tabon hankali a duniya, bayan da masu fama da cutar suka kai fiye da miliyan daya.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ana samun karuwa da masu dauke da wannan cutar musamman ma a kasashen Afrika ta yamma ciki har da nan gida Najeriya.
Haka zalika binciken ya sake bayyana cewar likitoci dari biyu ne ke duba kusan mutane miliyan dari biyu dake kamuwa da wannan cutar.
Wakiliyar mu Aisha Muhammad ‘Yanlema ta ttauna da kwararran likitan kwakwalawa na Asibitin koyar na Aminu Shehu Ibrahim Kano Dr, Aminu Ibrahim yayin da ake bikin ranar masu tabon hanakali ta duniya.