Manyan Labarai
Menene Alfanun Tafiye Tafiyen Shugaba Buhari?
Daga lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulkin Najeriya a shekarar 2015 shugaban kasar ya fara tafiye tafye zuwa kasashen waje.
Wadannan tafiye tafiyen da shugaba Buharin ke yi tun karbar ragamar mulki a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan makusanta shugaba Buharin ke alakanta tafiye tafiyen da shugaban ke yi da nemowa Najeriya makoma a sauran kasashen Duniya.
Tun farkon shekarar 2015 wato ranar 3 ga watan Yuni shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Niger domin tattaunawa da shugaba Muhammadu Issoufu a game da rikicin Boko Haram da ya addabi Najeriya kafin hawan shugaba Buharin mulki.
A zangon shugaba Muhammadu Buhari na farko ‘’yan kasa da dama na yiwa shugaban uzuri ganin cewa Gwamnatin ta sa jaririya ce,kuma tana bukatar lokaci domin a saita al’amuran Najeriya.
Daga cikin kariyar da makusanta shugaban kasar suka rika bayarwa har da nemawa Najeriya jari da habaka yanayin kasuwanci da kasashen waje.
Amma duk da wadannan dalilai da akai ta bayarwa har shugaban kasa Buhari ya kammala waadin sa na farko a matsayin shugaban kasa , suka daga bangarori musamman ma na ‘’yan adawa ke nuni da cewa tafiye tafiyen na shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kawo wa Najeriya alfanu ba .
Ko a kasafin kudi na shekarar badi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a farkon watan Oktoban da muke ciki na fiye da naira triliyan 10, har wasu masu fashin baki suke kallan kasafin kudin kasar na shekarar badi a matsayin lissafin dokin rano duba da yadda ba’a cika aiwatar da kasafin ba yadda ya kamata.
Ayyana kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buharin ya gabatar a matsayin lissafin dokin rano ya sa wasu ke ganin tunda har fitar da yake yi zuwa kasashen Duniya ba ta haifar da da mai ido ba , duk da yawon da shugaban yake yi zuwa wasu kasashen Duniyar domin inganta tattalin arzikin Najeriya.
Kididdiga ta nuna cewa a shekara ta 2015 kadai a watannin farko guda bakwai na hawan sa karagar mulki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasashen Duniya 16,inda a shekarar 2016 ya ziyarci kasashen Duniya 21.
A shekarar 2017 kuma shugaba Buharin ya ziyarci kasashe uku kacal ,sannan a shekarar bana shugaba Buhari ya kai ziyara kasashe uku idan kuma aka hada da ziyarar da yake yi a yanzu a kasar Saudi Arabia , shugaban ya ziyarci kasashe hudu ke nan ,daga shekarar day a hau mulkin zuwa yau a ka’idance shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasashe 47 kenan.
Wadannan tafiye tafiye da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi menene alfanun su ga ‘’yan Najeriya lokacin da waadin mulkin shugaban ya fara nisa.