Labaran Wasanni
Messi zai ci gaba da zama a Barcelona
Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi ya ce, zai ci gaba da zama a ƙungiyar, sabo da babu ƙungiyar da za ta iya ɗaukan sa kan kuɗin da aka sanya na siyan sa.
A cewar sa Messi, baya san wani abu da zai sanya su tsaya a kotu da ƙungiyar tasa ta Barcelona wanda hakan ne ya sanya shi yanke shawarar ci gaba da zama a ƙungiyar ta sa.
Messi, ɗan asalin ƙasar Argentina, mai shekaru 33 a duniya, a kwanakin baya dai ya bayyanawa ƙungiyar ta sa ta Bacerlona aniyar sa na son barin ƙungiyar.
Inda mahukuntan ƙungiyar ta Barcelona suka bayyana cewa duk ƙungiyar da ke son ɗaukan ɗan wasan dole ne sai ta biya kuɗin da suka tasamma 700m euro.
Tun daga lokacin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Munich ta lallasa ƙungiyar sa ta Bacerlona da ci 8-2 a gasar cin kofin zakarun turai na Champion League, wanda hakan ya zama mafi muni a cikin tarihin ɗan wasan na rashin nasarar da ya yi a wasa.
A kakar wasanni ta shekarar 2019/2020 da aka kammala ƙungiyar ta Barcelona ba ta samu nasarar ɗaukan kofi ba.
You must be logged in to post a comment Login