Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Middeslborough ta raba gari da Woodgate

Published

on

 

Kungiyar Kwallon kafa ta Middlesbrough ta sanar da raba gari da mai horar da kungiyar tsohon dan wasan kasar Ingila Jonathan Woodgate, ta re da mai da gurbin sa da Neil Warnock.

Korar tashi ta biyo bayan rashin nasarar da kungiyar tayi har gida a hannun takwarar ta ,ta Swansea da ci 3 da nema wanda hakan ya bar kungiyar a matsayi na 21 a kasan teburin gasar Ingila rukuni na biyu da yiwuwar fadawa rukuni na uku.

Kungiyar ta Boro, ta sanar da sallamar Woodgate a yau Talata tare da mai da gurbin sa da tsohon mai horar da kungiyar Crystal Palace Neil Warnock nan take.

Labarai masu Alaka.

Dele Alli zai fuskanci hukunci kan cutar Corona

An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona

Kungiyar ta godewa tsohon dan wasan nata da ya karkare Kwallon sa a kungiyar Woodgate tare da yi masa fatan alheri a gaba shekara guda bayan kama aikin sa a kungiyar a watan Yunin bara.

Zuwa yanzu haka Neil Warnock mai shekaru 71, zai gudanar da wasan sa na farko da Stoke City a ranar Asabar, ya dai raba gari da kungiyar Crystal Palace a watan Nuwambar bara bayan da kungiyar ta fada zuwa rukuni na biyu na gasar kasar ta Ingila.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!