Kiwon Lafiya
Ministan Ilmi Adamu Adamu ya fara zagayen cibiyoyin da aka ware don gudanar da jarrabawar JAMB
Ministan Ilmi na Najeriya Malam Adamu Adamu ya fara zagayen duba cibiyoyin da aka ware don gudanar da jarrabawar shiga manyan makarantun ta JAMB ta shekarar da muke ciki.
Lokacin da ya kai ziyarar gani da ido cibiyoyin Digital Bridge da Global Distance Learning a Abuja juma’ar nan, Malam Adamu ya bayyana wa manema labarai gamsuwar sa da iri shirin da cibiyoyin suka yi.
Ministan ilmin ya kuma yi kira ga daliban da za su zauna jarrabawar da su kara dagewa wajen koyon kwamfuyuta domin hakan zai taimaka musu wajen gudanar da jarrabawar yadda ya kamata.
Malam Adamu Adamu ya kara da cewa babu bukatar a samawa dalibai mataimaka yayin jarrabawar matukar daliban sun iya kwamfuyuta, kuma hakan zai taimaka musu gaya wajen gudanar da jarrabawar cikin sauki.