Labarai
Ministan kwadago ya sha alwashin fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi
Sabon Ministan kwadago da samar da aikin yi, ya sha alwashin tabbatar da cewa, an fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan.
A jiya Laraba ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministoci a zangon mulkin sa na biyu.
Da ya ke zantawa da manema labarai a gidan sa da ke Abuja, bayan karbar rantsuwa kama aiki, Dr Chris Ngige, ya ce, samun fahimtar juna tsakanin gwamnati da ma’aikata na daga cikin ayyukan da zai fi ba da fifiko a wannan karon.
Ya ce gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen ganin cewa ma’aikatan kasar nan sun kasance cikin walwala a ko da yaushe.