Addini
Muƙabalar malamai 6 da aka taɓa karawa a tsakanin malaman Kano
Yau Asabar ne za a gabatar da Muƙabalar nan ta Malaman Kano da Malam Abduljabbar Kabara, bayan shafe watanni biyar ana jira.
A watan Fabrairun da ya gabata ne, Gwamnatin Kano ta ɗauki matakin dakatar da malamin daga yin wa’azinsa.
Gwamnatin ta ce, ta yi hakan ne saboda yawaitar ƙorafe-ƙorafe game da kalaman malamin daga manyan malaman jihar.
A wata tattaunawa da Freedom Radio ta yi a kwanakin baya da shugaban majalisar malamai na Kano Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce, malamai a shirye suke domin wannan muƙabala.
Ƙarin labarai:
Za ayi zubeben kwarya tsakanin malaman Kano
Ko kaɗan umarnin kotu bai shafi muƙabala ba – Barista Fagge
Malam Ibrahim Khalili ya lissafo wasu zaman muƙabalar malamai shida da aka yi a baya.
An taɓa buga muƙabalar a zamanin Sarki Sanusi na ɗaya, lokacin da mutanen Ahmadiyya suka zo Kano.
An kuma ƙara yin wata a lokacin Maitatsine na farko.
Malam Khalil ya ce, haka ma an Gwabza tsakanin marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da marigayi Malam Auwalu Tal’udu, a masallacin Beirut Road.
Jama’ar Kano sun shaida yadda aka yi muƙabala tsakanin Dr. Tahar Adamu Baba Impossible da Malam Muhammad Bin Usman a baya.
Malamai sun zauna da Sheikh Yusuf Ali lokacin da ya ce, an ake wa Ubangiji wasiƙa.
An taɓa zama da marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam a fadar Sarkin Kano, kan ya ce, Ubangiji yana sama.
Yau ce ranar Muƙabala:
Da safiyar yau ne ake saran gudanar da wannan muƙabala, sai dai ba kamar yadda aka tsara tun a farko ba, Kwamitin shirya muƙabalar ya sanar da ƴan jarida da maraicen Jumu’a, cewa ba za a haska kai tsaye ba.
An amince ƴan jarida su shiga ayi a gabansu, sannan su naɗa domin yaɗawa daga baya.
Ma’aikatar al’amuran addini ta jihar Kano, ta ce, an yi kyakkyawan tsari tare da tanadar da jami’an tsaro domin tabbatar da tsari yayin zaman.
Ɓangaren zauren haɗin kan malaman Kano ta bakin sakataren su Dr. Sa’id Ahmad Dukawa ya ce, sun shirya tsaf.
Haka shi ma lauyan Malam Abduljabbar Barista Rabi’u Shu’aibu Abdullahi, ya ce, sun shirya tsaf domin wannan zama.
You must be logged in to post a comment Login