Labaran Wasanni
Muhammad Salah ne dan wasan Afrika da ya fi zura kwallo a gasar Firimiyar kasar Ingila
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah ya kafa tarihin zama dan wasan Afrika da ya fi zura kwallaye a gasar firimiyar kasar, inda a yanzu ya zarta Didier Drogba na kasar Ivory Coast.
Yanzu haka Salah dan asalin kasar Masar ya jefa kwallaye 107 a gasar ta firimiyar.
Mohammed Salah ya sha gaban Didier Drogba da ya yi wasa a Chelsea da ya kuma ci mata kwallaye da dama.
Sauran ‘yan wasan Afrika mafiya yawan kwallaye a gasar ta firiyar kasar Ingila sun hadar da Sadio Mane na tawagar kwallon kafar kasar Senegal da Liverpool mai kwallaye 100, sai Emmanuel Adebayor na Togo mai kwallaye 97, yayin da Yakubu Ayegbemi na Najeriya ke da kwallaye 95.
You must be logged in to post a comment Login