Labarai
Mun baza jami’ai 950 don bada tsaro a hutun Easter- NSCDC

Hukumar Tsaro ta Civil Defence NSCDC shiyyar jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta baza jami’anta su 950 a fadin jihar a kokarin ta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, yayin hutun Easter da gwamnatin tarayya ta ayyana.
Kwamandan hukumar, Muhammad Danjuma, ne ya sanar da hakan ta bakin shugaban sashen ayyuka na jihar, Jazuli Auza’i, ya ce.
Ya ce, hukumar ta tura jami’an ne daga sassa daban-daban na hukumar zuwa muhimman wurare, ciki har da cibiyoyin ibada da gine-ginen gwamnati da kasuwanni sai manya da kananan kantuna da tashoshi da sauran wuraren da mutane ke taruwa da kuma wuraren da ake zaton na iya zama hatsari.
Hukumar ta kuma bukaci hadin kan jama’a wajen bai wa jami’an tsaro goyon baya kafin da kuma yayin har ma da bayan bukukuwan.
You must be logged in to post a comment Login