Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar Civil Defence ta baza jami’ai 1,500 don bada tsaro yayin bikin Easter

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defense a jihar Kano, ta ce, ta bada umarnin baza jami’anta su dubu daya da dari biyar yayin gudanar da bukuwan Easter.

Mai magana da yawun rundunar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

DSC Ibrahim Idris ya ce, rundunar ta dauki matakin ne domin ganin an gudanar da bukukuwan na Easter cikin kwanciyar hankali da lumana musamman a wuraren da za a gudanarda shagul-gulan bikin a fadin jihar Kano.

Haka kuma ya kara da cewa, “A don haka rundunar na tabbatar wa mabiya addinin Kirista na Kano cewa ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a wuraren Ibadarsu har ma da sauran wuraren shakatawa domin nuna farin ciki da zuwan ranar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!