Labarai
Mun cafke matashin da ke iƙirarin sayar da kansa-Ibn Sina
Babban kwamandan hukumar Hisba a Kano Shurkh Muhammada Harun Ibn Sina ya ce sun yi nasarar cafke matashin nan da yake ikirarin sayar da kan sa.
Matashin mai suna Aliyu Idris dan asalin jihar kaduna ne, an cafke shi a ranar 27 ga watan Oktobar 2021
Matashin mai shekaru 26 a duniya a lokacin daya gurfana a gaban Hukumar hisba ya ce, yazo jihar Kano ne damin ganawa da mawaƙin nan Naziru Sarkin Waƙa sai dai bai samu ganawa da shi ba tsawon kwanani.
Inda yayi ta yawo a cikin Kano har guzurin sa ya ƙare hakan ta sa ya fara tunanin yadda zai yi ya koma gida.
Kwatsam sai yaje kasuwar kwari yana neman dako amma be samu ba, abinda ya sa ya yanke hukuncin sayar da kansa a farashin daya kai Naira miliyan 20.
Sai dai tuni natashin ya janye mudirin sayar da kan na sa bayan da hukamar Hisba tai masa nasiha.
You must be logged in to post a comment Login