Labarai
Mun cafke yan Daba fiye da 410- Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta cafke wasu daga cikin bata -garin da ta ke zargi da tayar da fadan daba a unguwannin Dan’agundi da Kofar Nai’sa, da yayi sanadiyyar raunata mutane da dama tare da janyo asarar dukiyoyi da dama.
Shugaban kwamitin kar-ta-kwana kan yaƙi da ayyukan daba da dawo da zaman lafiya da gyaran halin matasa, wanda gwamnatin Kano ta kafa Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio a yau Juma.
Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya ce, zuwa yanzu sun cafke fiye da ɓatagari 400 bayan fara aikin kwamitin, inda kuma a daren jiya suka cafke matasa 10 wadanda ke da hannu a fadan daba a unguwar Dan’agundi zuwa Kofar Na’isa.
Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya kara da cewa sun samu annan nasara ne sakamakon bayanann da suka samu na bata garin da ke haddasa tashe-tashen hankulan jama’a a tsakanin unguwannin na Dan’agundi da Sagagi da kuma Kofar Na’isa.
Latsa alamar Play a kasa domin sauraron muryarsa
You must be logged in to post a comment Login