Labarai
Mun cire rai: Babu alamun rage farashin wutar lantarki – Kwamared Dakata
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan cikar wa’adin makonni biyu na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, ba tare da samun sauyi ba.
A ranar 28 ga watan Satumban da ya gabata ne, ƴan ƙwadagon suka jingine shiga yajin aiki da zanga-zangar da suka kudiri aniya da cewar sun cimma matsaya har zuwa makonni biyu.
Ƴan ƙwadagon dai sun ƙudiri aniyar yajin aikin ne, sakamakon cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a kan farashin man fetur, abin da ya janyo farashin man ya ƙaru da kimanin kashi 11 cikin 100.
Sai kuma ninka farashin lantarki da gwamnatin ta yi.
Kwamared Kabiru Sa’id Dakata shugaban ƙungiyar tabbatar da adalci da bibiyar ayyukan gwamnati ta CAJA ya ce matuƙar aka ci gaba da tafiya a haka, to sai dai ƴan Najeriya su ci gaba da haƙuri.
Dakata ya ce alamu na nuni da cewa babu wani banbanci da za’a samu a gangaren farashin wutar lantarki, tun da ba’a yi wata nasara a bangaren rage farashin man fetur ba.
You must be logged in to post a comment Login