Labarai
Dalilan dakatar da hulda tsakanin bankuna da cibiyar kudi ta internet – CBN
Babban bankin kasa CBN ya ce ya dakatar da hulda tsakanin bankuna da cibiyoyin kudi da ke hada-hada ta kafar internet wato Crypto Exchanges ne sakamakon yadda tsarin ke tallafawa ayyukan ta’addanci da ke gudana a kasar nan.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin daraktan yada labaran bankin na CBN Osita Nwanisobi.
Sai dai ya ce haramta harka tsakanin bankuna da cibiyoyin kudin na Crypto Currencies bai shafi dukkannin huldodi na kudi ta kafar internet ba musamman Fintechs.
Ya ce tun da tsarin hada-hadar kudin na Cryptocurrencies bai da lasisi a Najeriya saboda haka ya sabawa dokokin bankin na CBN.
A cewar bankin na CBN kungiyoyin ‘yan ta’adda suna samun kudade ta hanyar hada-hadar ta Cryptocurrencies.
You must be logged in to post a comment Login