ilimi
Mun fitar da fiye da biliyan 100 don inganta fannin koyar da kimiyyar kula da lafiyar- TetFund

Asusun tallafa wa manyan makarantun gaba da sakandare na Najeriya Tetfund, ya ce, ya fitar da sama da naira biliyan 100 domin kara inganta fannin koyar da kimiyyar kula da lafiyar al’umma a wasu daga cikin manyan makarantu.
Shugaban Asusun Aminu Masari, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar Katsina.
Ya ce, hakan zai sa a magance karancin kwararrun ma’aikatan kula da lafiya da ake samu a fadin Najeriya.
Aminu Masari, ya kuma ce, a kowanne bangare na Najeriya an zabi jami’oi uku inda kowacce ta amfana da naira biliyan 4 domin yin gyara a fannin koyar da harkokin lafiyarta.
You must be logged in to post a comment Login