Labarai
Mun fitar da tsare-tsare don yaki da zazzabin cizon sauro – Dr. Aminu Ibrahim
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare a kokarin da take yi na yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a ya yin taron karawa juna sani akan yaki da zazzabin cizon sauro.
Dakta Tsanyawa ya kara da cewar kaso 25 na mace macen da ake samu a jihar Kano na da nasaba ne da cutar zazzabin cizon sauro don haka ya kamata duk kan al’ummar jihar da masu ruwa da tsaki su kara bayar da goyon baya wajan yaki da zazzabin cizon sauro a jihar.
Sanarwar mai dauke da sanya hannun jami’ar hulda da jama’a ta Ma’aikatar lafiya Hadiza Namadi ta kara da cewar Dakta Tsanyawa ya godewa dukkan Ma’aikatan lafiya bisa gudunmawar da suke bayarwa tare da cewar suna sanya ran nan da shekaru hudu gwamnatin jihar Kano ta za kara cimma nasara bisa yadda take kokari a bangaren na lafiya.
You must be logged in to post a comment Login