Labarai
Mun gaji da jiran na’urar Tracker – Ƴan Adaidaita
Direbobin baburan adaidaita sahu sun koka kan yadda har yanzu hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta Kano wato KAROTA, ta gaza cika alƙawarin sanya musu na’urar Tracker a cikin ababen hawan su.
Tun a bara ne dai hukumar ta fito da tsarin sake yin rijista lambar baburan na su, da kuma biyan maƙudan kuɗaɗe da nufin samar musu da na’urar Tracker wadda zata taimakawa hukumar wajen gano masu aikata laifuka a cikin su.
Sai dai har kawo yanzu, masu adaidaita sahun na ƙorafin rashin basu na’urar duk da yawan bibiya da suke yi.
Freedom radio ta tuntubi hukumar KAROTA ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa wanda ya ce, tuni hukumar ta samar da na’urar har ma ta aike da su zuwa kowacce ƙaramar hukuma.
A don haka yace a yanzu kowanne ɗan adaidaita ya koma zuwa ƙaramar hukumar sa ya bibiyi tasa na’urar don ya fara amfani da ita.
You must be logged in to post a comment Login