Connect with us

Labaran Wasanni

Shugabancin hukumar AFN ya dare gida biyu

Published

on

Mutane biyu na ikirarin lashe zaben shugabancin hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa AFN da aka gudanar daban-daban.

An dai gudanar da zaben ne a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, inda Shehu Gusau da kuma Tonobok Okowa kowane ke ikirarin cewa shi ne zababben shugaban hukumar ta AFN.

Hukumar ta kasance cikin rikicin shugabanci tun a shekarar 2019 sakamakon ‘yancin cin gashin kai da zababben shugaba na shekarar 2017 Shehu Gusau ya nema daga hannun ma’aikatar wasanni ta kasa.

Hakan ne ya sanya aka raba gari tsakanin shugaban hukumar Shehu Gusau da mataimakinsa Olamide George kowa na cewa shi ne shugaban hukumar.

An dai rantsar da shugabannin bangarorin biyu da zummar kama aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!