Labarai
Mun kama bindugogi 19 da alburusai fiye da 100 a mako biyu- CP Bakori

Rundunar Yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama bundugogi guda 19 da alburusai fiye da guda 100 a hannun wasu da ake zargin yan fashi ne da kuma masu aika laifuka da dama.
Kwamishinan yan sandan Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke yin holin makaman yau Laraba a shalkwatar rundunar ‘yan sanda da ke unguwar Bompai.
Kwamishinan ya kuma ce, rundunar ta samu nasarar kama miyagun kwayoyi da babura masu kafa uku da motoci wadanda barayi suka sace.
You must be logged in to post a comment Login