Labarai
Gwamnatin Jigawa ta umarci jami’an tsaro mata su sanya Hijabi

Gwamnatin jihar Jigawa, ta umarci jami’an tsaro mata da su rika sanya hijabi yayin da suke bakin aiki.
A wata sanarwa da ta fitar a baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta umurci wasu kamfanoni masu zaman kansu guda uku da ke aiki a jihar da su bar ma’aikatansu mata su sanya Hijabi yayin da suke kan aiki.
Majalisar zartaswar jihar ta bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan yada labarai, Sagir Musa, yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan kudurorin majalisar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse babban birnin jihar.
Haka kumaya bayyana cewa, wannan umarnin wani bangare ne na kokarin gwamnati na samar da yanayi mai kyau da walwala ga dukkan ‘yan kasa, musamman ma mata.
Sagir ya kuma ce, ana sa ran wannan mataki zai kara wa jami’an tsaro mata kwarin gwiwa a fadin jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa daukar matakin ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan Makarantu da Asibiti da tsaron Kotuna suka gabatar.
You must be logged in to post a comment Login