Kiwon Lafiya
Rashin shan isasshen ruwa na haifar da ciwon Koda-Dr Faruq Sabo

Wani likita a nan Kano ya shawarci al’umma da su rika shanruwa a kalla lita uku a rana domin kiyaye kansu daga kamuwa da cutar tsakuwar ƙoda.
Dr. Faruq Sabo kwararren likitan Koda a asibitin mafitsara na Abubakar Imam Urology ne ya bayyana haka.
Ya ce ana kamuwa da cutar ne sakamakon daskarewar wasu sinadarai dake cikin firsari, inda suke curewa waje daya a cikin koda su hanata aiki yadda ya kamata.
Likitan ya bayyana ƙarancin ruwa a jikin dan’adam a matsayin babban dalilin da ke janyo cutar tsakuwar ƙoda.
A karshe ya shawarci al’umma da su rika shan isasshen ruwa su kuma gujewa shan lemukan kwalba da abincin gwangwani domin kaucewa kamuwa daga cutar.
You must be logged in to post a comment Login