Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun rasa a ina kaso 50 na kudin dalibai yake zurarewa- SUG

Published

on

Kungiyar dalibai ta jami’ar Bayero ta Kano ta bukaci jami’ar kan ta binciki inda kashi 50 na kudaden da jami’ar ke cajar dalibai a matsayin kudin kungiyar ke makalewa.

A zantawar shugaban kungiyar dalibai ta SUG na jami’ar Sadi Garba Sa’id, da Freedom Radio ta wayar tarho ya ce, binciken da suka yi ne kan adadin dalibai da kuma kudin da jami’ar ke baiwa kungiyar suka gano cewa kaso 50 ake basu maimakon 100 na kudin.

Sadi Garba Sa’id, ya kara da cewa jami’ar na karbar naira 200 a hannun kowanne dalibi a matsayin kudin kungiya, sai dai sun gano naira 100 kadai ake baiwa kungiyar, a don haka ne suka bukaci makarantar ta bincika inda sauran kudin ke zurarewa.

Kungiyar daliban dai ta bukaci hakan ne a wata takarda da suka aike wa shugaban jami’ar mai dauke da sa hannun shugabannin da suka hadar da na kungiyar SUG ta jami’ar Sadi Garba Sa’id, da shugaban kungiyar dalibai Musulmi MSSN Lukman Usman Aliyu da kuma shugaban kungiyar dalibai ta ASO Fakhrudeen Auwal Taheer.

.An jima ana neman dalibai mata: BUK

Marigayi Alhaji Ado Bayero ne ya kafa makarantar sakandiren Dambatta

Marigayi Alhaji Ado Bayero ne ya kafa makarantar sakandiren Dambatta

Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.

Ta cikin takardar dai kungiyar daliban ta bukaci jami’ar ta janye batun Karin wasu kudade da ta yi ga dalibanta da suka hadar da kudin dakunan kwana da na wasu sauran caje-caje kamar yadda hukumar makarantar ta sanar ranar Juma’ar da ta gabata a makalarta ta mako-mako.

Bukatar kungiyar ta fito ne bayan kammala taron shugabanninta na kungiyoyin jami’ar wanda aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata, bayan da majalisar zartaswar jami’ar ta amince da yin karin kudaden a zaman da ta yi karo na 378 kuma aka wallafa sanarwar a makalar jami’ar.

Jami’ar ta Bayero, ta yi karin kudin dakunan kwanan daliban ne daga naira 12,150 zuwa naira 25,150.

Haka kuma Karin kudin ya shafi kudin kai tsaye kwasa-kwasan da dalibai masu digiri na farko daga naira 5,000 zuwa dubu 10,000.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!