Labarai
Mun Sahale dokoki guda 40 a majalisa ta 9- Majalisar dokokin Kano
Majalisar dokokin jihar Kano, ta ce, ta samu nasarar sahale dokoki guda arba’in tare da karɓar ƙudu Ƙudurori fiye da 200 daga mambobinta a tsawon shekaru huɗu.
Shugaban majalisar Engr. Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai bayan zaman majalisar ta 9 a yau Litinin.
Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ya ƙara da cewa, bayan haka kuma, majalisar ta samu ƙarin wasu nasarori da dama musamman waɗanda suka shafi ci gaban al’umma.
Ya ƙara da cewa, daga cikin dokokin da majalisar ta samu nasarar sahalewa akwai dokar kare hakkin kananan yara da dokar kafa hukumar gudanarwar majalisar sai dokar kashe kudaden majalisar da sauransu.
Shugaban majalisar, ya kuma yaba wa ma’aikatan zauren bisa irin gudummawar da suka bai wa ƴan majalisa har suka samu damar gudanar da ayyukansu cikin lumana da ƙaunar juna.
You must be logged in to post a comment Login