Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano

Published

on

Alƙalin alƙalan Kano mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta jagoranci rantsar da Engr. Abba kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan Jihar Kano.

Sabon gwamnan ya karɓi rantsuwar ne yau Litinin filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

An fara ne  rantsar da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Taron ya samu halartar sarakunan Kano da jagoran Jam’iyyar NNPP Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

Haka kuma ya samu halartar dubunnan ɗaruruwan magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya da suka yi shigar fararen kaya da jar Hula da jan kallabi da Hijabi.

Haka kuma, taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa da dama sauran manyan baki ne suka halarci bikin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!