Labarai
Yadda cutar Corona ta shigo Najeriya
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da bullar cutar nan mai saurin halakarwa wato Corona Virus wadda aka sauyawa suna zuwa COVID-19 a Najeriya.
Ministan lafiya na kasa Dakta Osagie Ehanare ya tabbatar da bullar cutar cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ta bulla ne a jihar Legas.
Shima Kwamishinan lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da bullar cutar, inda ya bayyana cewa wani dan kasar Italiya ne ya shigo da cutar.
Ya ce mai dauke da cutar dan kasar Italiya ya shigo Najeriya ne da nufin yin wani kasuwanci na dan wani lokaci tun ranar 25 ga watan Faburairu.
Inda ya ce mutumin ya kamu da rashin lafiya a ranar 26 ga Faburairu, inda a ranar 27 ga Faburairu ne aka tabbatar da mutumin yana dauke da cutar.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa tuni suka dauki matakan gaggawa wajen kare yaduwar wannan cuta, yana mai cewa mai cewa gwamnatin jihar Legas da guyiwa da cibiyar dakile cututtuka ta kasa don daukar matakin da ya dace.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu inda ya bayyana cewa zasu yi duk mai yiwuwa wajen dakile wannan cuta.
A cikin wannan sati da muke ciki an gwada wani dan kasar China a jihar ta Legas inda aka tabbatar da baya dauke da wannan cuta.
You must be logged in to post a comment Login