Labarai
Mun samar da hanyoyin bin diddigin amfani da miyagun kwayoyi- NAFDAC
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC, ta ce, ta samar da ingantattun hanyoyin bin diddigin abubuwan da ake amfani da su na muggan kwayoyi.
Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan lokacin da take kaddamar da shirin gwajin magunguna nau’in miyagun kwayoyi a Legas.
Farfesa Adeyeye ta ce an dauki matakin ne domin magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya, musamman a tsakanin matasa.
Ta ce an zabo magungunan narcotic a cikin wasu nau’ikan magunguna don rage shaye-shayen kwayoyi, tana mai cewa za’a yi amfani da wannan ga duk sauran kayayyakin da hukumar ta NAFDAC ta kayyade.
Ta ce daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya shi ne karuwar magunguna marasa inganci na jabu a Najeriya, matsalar da take kara tabar-barewa sakamakon raba magunguna ba bisa ka’ida ba da wasu marasa kishin kasa ke yi.
You must be logged in to post a comment Login