Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun san maboyar ƴan bindiga tsoron kashe fafaren hula ya sanya bamu gama da su ba – Lai Muhammed

Published

on

Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ya ce, gwamnatin tarayya tana iya kokarinta wajen ganin ta kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar kasar  nan.

 

Ya ce, cece-kucen da ake yi cewa gwamnati ba ta tabuka abin azo a gani kan matsalar tsaro ba gaskiya bane, domin kuwa nan ba da jimawa ba za a ga sakamakon ayyukan da gwamnati ta yi kan dakile matsalar tsaro.

 

Hakan na cikin wata sanarwa ce da ma’aikatar ta yada labarai ta fitar, tana mai cewa Alhaji Lai Muhammed ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Lagos.

 

Alhaji Lai Muhammed ta cikin sanarwar dai ya kuma ce gwamnati tana sane da maboyar ‘yan bindiga kawai dai tana bin hanyoyin da doka ta tanada ne domin gudun amfani da karfi da ya wuce kima wanda sanadiyar haka ya janyo rasa rayukar fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!