Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kaddamar da sabon masallacin sarkin musulmi a Kano

Published

on

Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya ja hankalin al’ummar musulmi da su ji tsoron Allah cikin al’amurran su na yau da kullum don samun tsira.

Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi jan hankalin ne ta cikin hudubar sallar juma’ar da ya jagoranta a masallacin juma’a na Sultan Abubakar na uku da ke karamar hukumar Gezawa a nan Kano.

Haka kuma Sarkin ya bukaci musulmi da su kara riko da sunnar fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W.
Wakiliyarmu Aisha Shehu Kabara da ta yi sallah a masallacin ta ruwaito cewar yau ne aka bude masallacin na Sultan Abubakar na uku a garin Gezawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!