Labarai
Mun shirya kawo ci gaba a ƙungiyar mata ƴan jarida – Aisha Bura
Sabuwar Zaɓaɓɓiyar shugabar ƙungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta alkawarta yin tafiya da kowanne ɓangare domin samar da haɗin kai da ci gaban mambobin ƙungiyar.
Hajiya Aisha Bura ta bayyana hakan a ranar Lahadi, jim kadan bayan kammala rantsar da ita a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a daren ranar Asabar.
Ta ce, akwai buƙatar mambobin ƙungiyar su bata haɗin kai don ganin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
“Za mu mutunta kowa mi yi tafiya da kowa, mu kuma bada horo ga mambobinmu domin su samu ƙwarewa” a cewar Bura.
Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta samu nasara da kuri’u 498 yayin da abokiyar takarar ta kuma shugabar kungiyar mai barin gado Hajiya Ladi Bala ta samu kuri’u 381.
Tun a ranar Asabar ne aka buɗe babban taron ƙungiyar NAWOJ karo na 11, kuma a daren ranar ne aka yi zaɓen sabbin shugabanni, wanda mambobin ƙungiyar daga jihohin ƙasar nan 36 da birnin tarayya Abuja suka samu halarta.
Kuma zaɓen ne ya baiwa Hajiya Aisha Ibrahim Bura nasara tare da sakatariyar ƙungiyar Wasika Kadan da sauran ƴan takara.
You must be logged in to post a comment Login