Labarai
Mun shirya yakar ‘yan siyasa masu furta kalaman tunzuri – Kungiya
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin al’umma a nan Kano ta ce, ya zuwa yanzu ta kammala shirin yakar duk wani dan siyasa da ke furta kalaman da za su iya haifar da hargitsi a babban zaben kasa na shekarar 2023.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Kwamared Ibrahim Wayya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio a safiyar ranar Litinin.
Kwamared Ibrahim Wayya ya kuma ce, kungiyar ta fito da tsarin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan takarar gwamnan Kano saboda tabbatar da yin zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.
kungiyar ta ce, ta kula da cewa a halin yanzu mutane suna cikin tashin hankali da musifa na rayuwa, wanda suke ganin kalaman za su iya tunzura su, wanda zai zama kamar tsokana ce ga al’ummar kasar nan.
Don haka suke ganin hakan ka iya haifar da hargitsi da zai kai ga tashin hankula, da asarar rayuka, da dukiyoyi.
kwamred wayya ya ce wajibi ne a dakile wannan matsalar, don kiyaye abinda ka iya zuwa ya dawo a lokacin zabe.
You must be logged in to post a comment Login