Labarai
Mun tara fiye da Tiriliyan guda a matsayin kudaden haraji – FIRS
Hukumar tattara kudaden shiga ta kasa FIRS ta ce ta tara kudi kimanin naira tiriliyan 1 da biliyan 2 a matsayin haraji a zango na biyu shekarar da muke ciki.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taronta na zango na biyu.
Ta kuma ce harajin ya ragu idan aka kwatanta da zango na biyu na shekarar da ta gabata, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 1 da biliyan 4.
Sanarwar ta kara da cewa jadawalin tattara harajin ya nuna cewa bangaren harajin hukumar samar da man fetur ya samu naira biliyan 440, wanda ya samu kari mai yawa kan yadda aka yi kiyasi na naira biliyan 71.
Wanda wadansu banagarorin harajin da ba na man fetur ba suka samu ragi daga jadawalin da aka yi kiyasi na naira tiriliyan 1 da biliyan 1, inda ya dawo naira biliyan 848 cikin zango na biyu.
Sanarwar ta kara da cewa harajin kamfanoni ya kai naira biliyan 324.3 wanda kuma bangaren iskar iskar Gas ya tattara naira biliyan 77 da biliyan 7.
You must be logged in to post a comment Login