Labarai
Muna aikin samar da “Mobile Transformer” a garin Bichi – TCN
Kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa TCN yace yunkurin da suke yi na samar da babbar transformer (mobile transformer) a Bichi da zata rika bai wa kusan kananan hukumomi bakwai wuta zai taimaka wajen farfado da kamfanoni tare da inganta tattalin arziki.
Babban daraktan kamfanin Injiniya Sule Ahmed Abdul’aziz ne ya bayyana hakan, lokacin da suka kai ziyara fadar gwamnatin Kano.
Ya Kara da cewa samar da transformar zai taimaka wajen samar da ayyuka ga matasa.
Da yake jawabi a yayin ziyarar dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi Abubakar Kabir Bichi, yace da zarar an kammala ginin wajen ajiye transforma din to za a dauko ta a kawota Bichi domin a fara hadata.
Sannan yace za kuma ta taimaka wajen samar da ruwa a yankunan Bichi, da tsanyawa, Kunchi, tofa da sauran su.
Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa da yake jawabi gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace wannan al’amari ne mai kyau musamman ma yadda zai farfado da tattalin arziki a wannan yanayi da ake ciki na Corona adon haka ya bada tabbacin kula da transformar yadda ya kamata da zarar an kammala hadata.
You must be logged in to post a comment Login