Connect with us

Labarai

An janye wa Magu jami’an tsaron da ke bashi kariya

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta janye jami’an tsaron da ke aiki a gidan dakataccen shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da kuma wadanda ke bashi kariya.

Rahotanni sun ce an kuma kwashe dukkanin motocin da ke gidan Ibrahim Magun a unguwar Maitama da ke Abuja.

A ranar Litinin din da ta gabata ne jami’an tsaron farin kaya suka yiwa dakataccen shugaban hukumar na EFCC rakiya zuwa ofishinsu da ke Abuja, kuma daga lokacin ne ya fara bayyana gaban kwamitin bincike na fadar shugaban kasa sakamakon zargin aikata rashawa da ake masa.

Tun daga lokacin ne kuma aka cigaba da tsare Ibrahim Magun a birnin tarayya Abuja. Ko da yake a ranar Juma’a ce Magun ya nemi babban sufeton yan sandan Najeriya ya bayar da belinsa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!